Babangida Ya Ce Shi Bai Ce Kar A Zabi Buhari A 2019 Ba

  • Ibrahim Garba

CHINA NIGERIA DIPLOMACY

A cigaba da cece-kucen da ake yi game da makomar siyasar Najeriya a 2019, tsohon Shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida (murabus) ya nesanta kansa daga zargin cewa ya yi kira ga 'yan Najeriya da kar su zabi Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Da alamar tsohon Shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (murabus), ya nesanta kansa daga wata wasikar da mai magana da yawunsa, Prince Kassim Afegbua ya danganta ta da shi. Wasikar, wadda ke nuna cewa Babangida ya nuna bai son a sake zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta janyo murza gashin baki a fagen siyasar Najeriya.

Kodayake babu inda wasikar ta fito karara ta nuna cewa Babangida bai son a zabi Buhari, akalla akwai jirwaye mai kamar wanka game da wannan batu a wasikar. Hasalima a wani babi mai taken THINKING ALOUD (Wata Tunani Mai Zurfi) a wasikar, biri ya yi kama da mutum game da rashin son Buhari ya sake tsayawa takara. A wannan babin an nuna kamar Babangida na cewa “Ya kamata mu bai wa Shugaba Muhammadu Buhari hadin kai don ya kammala wa’adinsa mai cika ran 29 ga watan Mayun 2019 sannan mu yi sharar fage ga sabbin shugabannin da za su jagoranci kasar.”

Babangida, a cewar marubucin, ya kara da cewa, “A yayin da na ke wannan bayanin, ba wai ina hana Shugaba Buhari ‘yancinsa na yin zabe da kuma na a zabe shi ba ne, to amma akan shiga wani irin lokaci a rayuwar kowace kasa wanda lokaci ne da ya kamata a fifita Muradin kasa bisa na kai.”

Wasikar ta kuma tabo tashe-tashen hankulan da Najeriya ke fama da su, inda ta danganta Babangida da cewa, “Kama daga Kudancin Kaduna zuwa Taraba, daga jahar Binuwai zuwa jahar Rivers, daga Edo zuwa Zamfara, jina-jina ake ta yi. A garin Dansadau na jahar Zamfara, kwanan nan aka yi asarar rayuka sama da 200 babu gaira babu dalili. Kisan kiyashin da aka yi a Binuwai ma ya sa na fara tambayar anya wannan ce kasar da wasunmu mu yi yakin tabbatar da kasancewarta kasa guda…. Yanzu akan bayyana Najeriya da kasar da jini ke malala kamar ruwan kogi…”

To sai dai a wata wasika mai dauke da sa hannun Babangida da kansa, wadda wasu kafafe su ka rabar, tsohon Shugaban ya musanta kalaman da kakakin nasa ya danganta shi da su. Ya ce, “Ya ku ‘yan jarida …. barin in gaya ma ku dalla-dalla cewa a matsayina na tsohon Shugaban Kasa kuma dattijo, ina da cikakken sukunin ganawa da hukumomi na can sama ba tare da na bi ta hanyar janyo cece-kuce a bainar jama’a ba. Saboda haka, kalaman da aka fada a can (wato a waccen wasikar) ra’ayi ne na marubucin kawai."

To saidai a wasikar nesanta kansa daga wasikar da Kassim ya rattaba wa hannu a madadinsa, Babangida ya nuna damuwarsa game da tabarbarewar yanayin tsaro a Najeriya.