Tsohon shugaban Nigeria Ibrahim Badamasi Babangida da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun kaddamarda kyamfen din tsayawa zaben shugaban kasa na 2011.
Tsohon shugaban Nigeria, Ibrahim Badamasi Babangida, ya fito fili, ya kaddamarda niyyarsa na yin takaran shugaban kasar Nigeria din a zabenta na gaba da za’ayi a 2011. A cikin kalaman da yayi a yau Litinin ne, aka ji General Babangida yana cewa tunda dai jam’iyyarsa ta PDP tace kowa yana da damar ya tsaya takaran, hard a shugaba maici yanzu Goodluck Jonathan, to shima zai gwada tasa sa’ar. A jiya ne shima tsohon VP Atiku Abubakarya kaddamarda nashi kyamfen din na neman mukamin shugaban kasan a badi. Fitowar wadanan muhimman mutanen biyu ance ta zama abin damuwa ainun a wurin shugaba Jonathan wanda shkma ake sa ran ya fito takara badi din.