Bukin wannan shekara mai take kamar haka, Sauyi Zuwa ga Al’umma Mai Dorewa da Jimiri, ya mai da hankali ne a kan samar da yanayi da zai bada dama ga kawo sauyin da zai kai ga cimma ajenda ci gaba na muradun karni da ake hasashen a shekarar 2030.
Bukin na wannan shekarar ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su karfafa jimirin al’ummarsu masu fama da nakasa ta hanyar samar da gine gine a birane da inda mutane ke zaune, su kuma magance musu matsalolin da canjin yanayi ke haddasawa, kana su dauki matakai agaza musu yayin wani bala’i.
Mutanen da ke fama da matsalar nakasa a Najeriya, sun yi kira ga hukumomi da suka rika waiwayar matsalolinsu domin su ma a rika damawa da su a harkokin yau da kullum. Kan haka ne kuma wakilin Sashen Hausa Hassan Umaru Tambuwal ya tattauna da wani mai larurar.
Your browser doesn’t support HTML5