Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu wata hanya da za’a iya wanzar da zaman lafiya a Syria matukar Shugaba Bashar Al-Assad ne ke shgabancin kasar.
A wani bayani da tayi wanda za’a nuna shi a yau lahadi a gidan talabijin na CNN, Nikki Haley tace “ Babu wata hanya da ta rage da za’a bi a siyasance domin warware matsalar Syria matukar Assad shine ke rike da gwamnatin.”
A wani bangaren kuma Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson cewa yayi ruguza daular Da’esh wacce aka fi sani da ISIS shine mafi muhimmanci a Syria.
Sakataren ya fadi haka ne a yayin wata tattaunawa da akayi dashi a wani shiri na gidan Talabijin na CBS mai suna (Face Of The Nation) a turance inda yace “Abu mafi muhimmanci na farko shine murkushe ISIS” Sannan “Da zarar an rage barazanar da ISIS ke yi ko kuma murkushe su baki daya, ina kyautata zaton zamu iya maida hankalin mu waje daya kan daidaita al’amurra a Syria.”
A jiya Asabar jiragen yakin Syria suka ci gaba da tashi a filin da Amurka ta kai harin makamai masu linzami a ranar juma’ar da ta gabata, A cewar gwamnan yankin wanda ya bayyana cewar sansanin na aiki ne “cikin sauri.”
Bayanin na gwamnan Homs Talal Barazi yazo ne daga Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ‘Yan awanni bayan Gwamnatin Syria ta bada sanarwar Harin da Amurka takai na makamai masu linzami a kan filin jirgin na Shayrat ya lalata wani yanki na filin.
Masu sa’ido daga Kungiyar kula da hakkin dan Adam dake Syria sun ce jiragen yaki sun sami damar tashi daga filin a ranar ta Jumma’a domin kai hari kan Yan tawayen dake gabashin yankin.