Ba Za a Yi Amfani Da Na'ura Mai Taimakawa Alkalin Wasa A UEFA Ba -Inji Aleksander Ceferin

Shugaban Hukumar kula da wasannin kwallon Kafa ta nahiyar turai ya ce UEFA ba za ta yi amfani da Mataimakin alkalin wasa na (VAR) ba a gasar zakarun Turai na shekara mai zuwa saboda "rikice-rikice" da ke kewaye da shi.

Ita dai wannan na'ura ana amfani da ita ne wajan taimakawa alkalin wasa ya yayinda wani abu ya faru wadda alkalin wasa bai gani ba ko bai fahinta ba musamman wajan jefa kwallo a raga.

Aleksander Ceferin, wanda shine shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, ya fadi hakanne ranar Litinin a taron majalisar wakilai ta UEFA da ake yi duk shekara inda wannan karon aka gudanar a kasar Slovakia, ya ce har yanzu ba'a gama fahintar yadda abun yake aiki ba, don haka Har yanzu akwai rikice-rikice, tattare da na'urar.

Shugaban ya kara da cewa ba wai yana kushe na'urar bane amma yana bukatar a fahinci amfani da ita. Aleksander ya ce za a sa ido domin a gano abun sosai a gasar cin kofin duniya, "2018 da za'a yi a kasar Rasha.

An yi amfani da VAR a wannan kakar a wasanni a lig daban-daban, ciki har da Bundesliga, Jamus da Serie A. Italiya. da ma wasu wasannin a wasu kasashe.