Ba Za'a Kidaya Kuri'ar Runfar Da 'Yan Banga Suka Hana Amfani Da Na'ura Ba

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ba da tabbacin za a fara gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun dokoki a ranar Asabar 9 ga wata a dukkan fadin Najeriya a lokaci daya.

Hukumar ta kara da cewa za a tabbatar da amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a, a dukkan mazabun da za a gudanar da zaben a jihohi 29.

An ruwaito kwamishinan labarun hukumar Festus Okoye na cewa duk rumfar da ‘yan banga su ka hana jami’an zabe amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a, za ta rasa samun kidaya kuri’un ta.

Shugaban hukumar zaben Mahmud Yakubu, ya bayyana yawan masu rijista da runfunan zabe a fadin Najeriya, “idan ka dauki takardar kada kuri’a kawai, mun buga dai-dai-dai har miliyan dari hudu da ashirin da daya”

‘Yan siyasa na bayyana ra’ayin su kan irin tasirin da su ke ganin wadanda su ke marawa baya za su yi a zaben.

A na kuma sa ran zabe a jihar Zamfara ya gudana cikin lumana, ya na mai cewa fitowar manyan ‘yan takara a zaben shugaban kasa daga Arewacin Najeriya mai jihohi 19 ya kawo saukin lamurra.

Masana na cewa zaben kan iya ba da mamaki don yiwuwar samun kujeru a wasu yankuna ga sababbin kananan jam’iyyu baya ga manya irin APC, PDP da AFGA.

Ga rahoton wakilin shashen Hausa na Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya daga birnin Tarayya.

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Za'a Kidaya Kuri'ar Runfar Da 'Yan Banga Suka Hana Amfani Da Na'ura Ba 2'40"