Gwamnatin Najeriya ta soke matakin bude makarantu ga daliban da zasu rubuta jarabawar WAEC a wannan shekarar.
WASHINGTON, D.C. —
Ministan harkokin ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da yayi da manema labarai da yammacin yau.
Adamu ya ce makarantu ba zasu bude ba har sai an tabbatar da cewa Covid-19 ba za ta iya yi wa dalibai illa ba.
Ya kara da cewa, babu makarantar da za ta yi WAEC a Najeriya a wannan shekarar.
Hakan na zuwa ne bayan da Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana a ranar Litinin cewa za a gudanar da WAEC a cikin watannin Augusta da Satumba.