NAJERIYA: Ba Wani Kudi Tsakanina Da Sambo Dasuki, Inji Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa

Yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin abinda gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari. Domin kuwa a cewar ita sabuwar gwamnatin ta Buhari, sun sami kasar a gurgunce saboda illar da wawaso da babakere ya yi mata ya hana kasar motsi.

An sami badakalar da ta taso wacce ke da alaka da matsalar al’mundahana da dukiyar kasa wacce ta ja har aka cafke Kanar Sambo Dasuki mai ritaya kuma tsohon mashawarcin Shugaban Najeriya zamanin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da ya sauka bayan kayin da Shugaban Najeriya na yanzu Muhammadu Buhari yayi masa.

Wannan kamu na Sambo ya zame wata allura data tono garma har ta giggirbi manyan Najeriya da dama, ciki har da tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa. Inda shima wannan guguwar ta kwasa da shi har gaban hukumar EFCC masu yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya. Bayan kwashe kwanaki a hannunsu aka rankaya kotu a kasar, daga baya aka bada belinsu.

An ta yama didi da maganar cewa shima bafarawa ya karbi makudan kudaden da suka kai Miliyan Dubu Hudu Da Dari Shida, da aka ce yace ya karba ne don rabawa Malamai a kokarin samun nasarar zarcewar tsohuwar gwamnatin kasar.

A karshe dais ashen Hausa na Muryar Amurka ya zakulo tsohon Gwamnan inda ya bayyana mana iyakar abinda ya sani a hirarsa da abokin aikinmu Yusuf Aliyu Harande.

Your browser doesn’t support HTML5

NAJERIYA: Ba Wani Kudi Tsakanina Da Sambo Dasuki, Inji Bafarawa - 4'00"