Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Virgil Van Dijk
ya bayyana cewa, shi kadai ba zai iya tunkarar dan wasan Barcelona Lionel Messi ba a wasan da za su yi ranar 1 ga watan Mayu 2019, cikin gasar cin kofin zakarun Turaia matakin wasan daf da na karshe Semi Final, inda zasu ziyarcesu a Camp Nour karawar farko.
Van Dijk yace yana tsammannin cewa, akwai bukatar hada karfi da karfe kafin tare dan wasan Messi wanda a bana ya zurara kwallaye har guda 45, a wasannin daban daban da ya buga wa kungiyarsa wanda suka hada da kwallayen da ta taimaka wajen samun nasarar zagayen gaba azakarun Turai.
Bayan haka kuma Messi gwarzon dan wasan kwallon kafa ne a duniya, amma dai a zura idanu don ganin yadda za ta kaya a wasan nasu wanda zai kasance na hamayya.
Van Dijk ya kasance dan wasan baya mafi tsada a duniyar tamola, Liverpool ta sayo shine daga kulob din Southampton akan zunzurutun kudi har fam
miliyan £75.
Haka zalika yana cikin 'yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan bana a kasar lngila.
Liverpool dai tana mataki na daya a saman teburin firimiya lig na Ingila da maki 85, inda Manchester City ke biye da ita damaki 83, a ranar Lahadi mai zuwa zata fafata da Cardiff City cikin wasan mako na 35.