A wata zantawa da Muryar Amurka ta yi da tsohon gwamnan mallam Isa Yuguda, ya bayyana cewa wannan batu ba haka yake ba, domin kuwa har ya zuwa yanzu yana da rufin asirinsa, kuma ya fara aikin tonon ma’adanai ne domin ya nemi halal din sa.
Mallam Isa, ya bayyana cewa shi da kansa ya dauki hoton bidiyon ya aika kafar sada zumunta, domin ya zaburar da matasa su mike domin neman na kansu, ganin cewa ya rike manyan mukamai a rayuwarsa hakan bai hana shi yin amfani da karfinsa wajen neman halal.
Tsohon gwamnan dai ya yi ayyuka da suka hada da Ministan Sufuri da zama Manajan Daraktan Bankunan Najeriya, kafin daga baya kuma ya zama gwamnan jihar Bauchi har na tsawon shekaru takwas.
Bayan saukarsa daga kujerar gwamna, kamar yadda ya fadawa Muryar Amurka, ya koma gonarsa ne da gwamnatin tarayya ta bashi tun asali wadda ke dauke da ma’adanai, ya kuma ci gaba da aikin hako ma’adanai.
Saurari cikakkiyar hirar Abdulwahab Muhammad da Mallam Isa Yuguda.
Your browser doesn’t support HTML5