Mai horar da ‘yan wasa na kungiyar kwallon kafa na Manchester United, Jose Mourinho, yace baya da masaniyar ranar da dan wasan tsakiyar kulob din Paul Pogba, zai dawo filin wasa daga jinyar da yakeyi na kafarsa.
Dan wasan ya samu rauni ne tun a ranar 12, ga watan Satumbar da ta ne, a wasan da kungiyarsa ta Manchester tayi da Kungiyar Basel, na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) a matakin wasan rukuni,
Lokacin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida Mourinho, yace shi bai san halin da dan wasan yake ciki ba dangane da dawowansa fili domin bashi yake kula da bangaren lafiyarsa ba akwai wanda hakkinsu ne,
Amman dai yasan ko Paul Pogba, nanan ko bayana yana da karfin gwiwar cewa ‘yan wasan da yake dasu zasu kai kungiyar ta Manchester United ga samun nasara a wasanninta,
Pogba dan kasar Faransa wanda ya zo kungiyar ta Manchester a 2016, daga kungiyar Juventus akan kudi fam miliyan £89, yanzu haka ya komo Carrington din, daga Miami, amma Mourinho ya bayyana cewa dan wasan ba cikin da tawagar farko, na yan wasan Manchester United.
Your browser doesn’t support HTML5