Rahotanni daga jahar Maiduguri na nuna cewar a sakamakon wasu hare haren da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai ranar laraba da ta gabata a birnin Maiduguri, rundunar sojin jahar ta bada sanarwar kafa dokar ta baci a jiya Alhamis sa’annan yau kuma ta kara tsawaita dokar wadda ba’a san lokacin da za’a janye ta ba.
A wata hira da Mahmud Lalo yayi da Haruna Dauda, ya bayyana cewar jama’a da dama na korafe korafen cewar yanzu fa lokacin mulkin farar hula ne amma doka irin wannan tana fitowa daga hukumomin sojin jahar, a maimakon rundunar tsaro ta ‘yan sandan jahar kokuma ofishin gwamnatin jahar, kuma a cewar sa, wanna doka ta haramta fita ne gabaki daya kuma duk da cewar rikicin ya lafa, kuma jami’an basu fadi dalilin kara tsawaita dokar ba.
Koda shike da farkon kafa dokar, jami’an sun bayyana cewar an sa dokar ne a sakamakon yin sahihin bincike kan wasu mata da sukai yunkurin shiga garin na Maiduguri dauke da bama bamai wandan da sukayi anfani da su wajan kai harin da suka yi na ranar laraba.
Jama’a dai na korafin ne saboda a cewar su, harin ya tsaya ne a wajen gari dan haka bai kamata a takura su ba, ya kamata jami’an tsaron su bar jama’a su cigaba da ayyukan su, su kuma jami’an su koma yankunan da abin ya afku domin fuskantar su. Yanzu haka sojoji ne kadai ke rangadi a hanyoyin garin kuma duk wanda suka gani a hanya jiki magayi.
A halin yanzu dai ba'a sami adadin mutanen da suka rasa rayukan su ba sai dai akwai alamun cewar akwai jami'an soji biyu wadanda suka sami raunika, da kuma wasu jama'a da ke asibitoci suna amsar magani.
Ga rahoton Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5