Shugaban Kwamitin Neman Sulhun yace sun shiga Bama sun taras ana wannan ba-ta-kashin ne, amma bai hana su yin abubuwan da suka kai su can ba.
Shugaban kwamitin neman sulhunta rikice-rikicen dake faruwa a arewacin Najeriya, kuma ministan ayyuka na musamman, Barrister Kabiru Tanimu Turaki, yace babu gaskiya cikin rahotannin dake cewa sun tsallake rijiya da baya lokacin da aka kai ma tawagarsu hari a garin Bama.
Ministan yace wannan fadan da ake magana bai ma shafe su ba, domin sun shiga garin ne sun taras ana gwabza wani fada a tsakanin dakarun tsaro da wasu 'yan bindiga 'yan tsiraru.
Yace sun samu sun gudanar da dukkan ayyukan da suka kai su garin na Bama, ciki har da ziyarar mai martaba Shehun Bama, da duba gidaje da kantunan da aka kona a lokacin farmakin da 'yan bindigar Boko Haram suka kai kan garin a cikin watan Mayu.
A hirarsa da wakilin Sashen Hausa, Haruna Dauda, shugaban kwamitin yace abinda ya faru ba shi zai hana kawo sulhu ba, kuma ko da ma za a iya cimma sulhu, irin wadannan kananan abubuwa ba za a iya kawar da su baki daya ba, domin tana yiwuwa a samu wani ko wasu 'yan kalilan da zasu ce su ba su yarda ba.
Haka kuma yace gwamnati ta bayar da umurnin a saki wasu mutane, akasarinsu mata da yara, wadanda aka kawar daga gidajensu lokacin fadan da ake yi. Yace ba tsare wadannan mutane aka yi ba, an dai kawar da su ne domin kada fada ya rutsa da su.
Ga cikakkiyar hirar Barrister Kabiru Tanimu Turaki da Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5