Ya zuwa yanzu dai babu wani matsayi da a ka cinma, a kan yawan jama’a da za su halarci kallon wasannin gasar Firimiya. Manyan jami’an shirya wasan na duba yuwuwar hana gaisawar ‘yan wasa gabanin fara wasa.
Sai dai ana tunanin babu wani dan wasa da zai gaisa da takarawarsa. Bisa al'ada akan gaisa kafin a fara wasa.
Annobar cutar Coronavirus na neman sa manyan kungiyoyin wasan Firimiya daukar matakan buga wasa batare da ‘yan kallo sun halarci wasan a cikin filin wasa ba, a cewar wani babban jami’in kungiyar Everton Sasha Ryazantsev.
An samu barkewar cutar ta Coronavirus a kasar ta Ingila, inda fiye da mutum 100 suka kamu da ita a ranar Alhamis.
Wasu kasashen duniya sun dakatar da duk wasu wasannin motsa jiki, don takaita yaduwar cutar, wanda kasar Italiya na daya daga cikin irin wadannan kasashen da suka dakatar da duk wasu ayyukan wasanni.