Ba Mamaki Najeriya Ta Karbi Bakoncin Kwallon Duniya

Sunday Akin Dare, Ministan Matasa da Wasanni

Muna sa ran kaiwa karshe da hukumar FIFA ko Najeriya zata karbi bakoncin gasar kofin duniya ta mata.

Ma'aikatar matasa da cigaban wasanni ta Najeriya na daf da tattaunawa da Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Duniya (FIFA) kan batun karbar bakoncin gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 20 da haihuwa ajin Mata.

Ministan matasa da ci gaban wasanni, Mr. Sunday Dare ne ya bayyana hakan a Abuja, yayin da yake zantawa da manema labarai, bayan wata ziyarar aiki da suka kai shi da takwaran sa Ministan Babban Birnin Tarayya a filin wasa na MKO Abiola.

Dare yace tawagar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, sun kasance a Najeriya wani lokacin a watan Agusta, domin duba kayayyakin da ake dasu, kuma zasu dawo nan bada dade wa ba.

Bayan haka Ministan yace ana nan ana gina gari guda daya da za'ayi masauki, watakila zai iya yuwa a jihar Legas.

Ya kara da cewa hukumar NFF da ma'aikatar wasanni suna nazari kan wasu daga cikin bukatun da FIFA ke da, wanda suka shafi wajen atisaye goma sha daya, manyan filaye biyu, da wasu 'yan abubuwa na kiwon lafiya, tsaro, da kuma na sadarwa.

Saboda haka nan da wani lokaci za'a tattaunawa da FIFA, domin samun fahimta a tsakani daga yanzu zuwa Janairu.

Kuma za'a duba a takaitaccen lokaci sannan daga baya a yanke hukunci tare da FIFA, ko Najeriya a shirye take ta karbi bakoncin gasar.

Ya ce ma'aikatarsa da hukumar NFF ta Najeriya suna aiki kafada da kafada, domin biyan bukatun FIFA na karbar bakoncin gasar biyo bayan sakamakon da hukumar kwallon kafa ta bayar a baya.