Ba Mamaki Gareth Southgate, Ya Zamo Kocin Manchester United

Gareth Southgate

Wasu rahotanni na nuni da cewar da yuwar Manchester United ta ba kocin kasar Ingila Gareth Southgate, aikin mai horar da 'yan wasanta domin maye gurbin Jose Mourinho, da ta sallama a watan Disambar shekarar 2018.

Inda ake rade-radin cewar Southagate zai karbi ragamar aikin a hannun Ole Gunnar Solskjaer, wanda ke rikon kwarya a matsayin kocin kungiyar zuwa karshen kakar wasan bana.

Southgate mai shekaru 48 a duniya, ya taka rawar gani a gasar cin kofin duniya na 2018 da ya gudana a Rasha, inda ya kai tawagar Ingila wasan daf da karshe, sannan ya samu nasarar kaiwa wasan daf da karshe a wasannin Nations League tare da tawagar Ingila.

Wannan rahoton na zuwane bayan da wasu ke ganin cewar da wuya kocin Tottenham Mauricio Pochettino, ya bar kulob din dan tahowa Old Trafford kamar yadda kungiyar ta bukaceshi.

A kwai wadanda ake alakantasu da aikin horas da 'yan wasan Manchester United, wanda suka hada tsohon kocin Real Madrid, Zinedine Zidane da kocin Juventus, Massimiliano Allegri.

Sai dai kuma kocin rikon kwarya Solskjaer na fatan a ba shi aikin na din din din, bayan da ya ci wasa shida a jere a kungiyar, inda a ranar Lahadi da ta gabata United ta doke Tottenham daci 1-0 a gidanta bangaren firimiya lig.

Hakan ya sake bashi karfin gwiwa a tarihin kungiyar Manchester na kasancewa shine mai horas da 'yan wasa na farko a kulob din da ya ja ragamar wasannin 6 a jere, duk yana samun nasara daga farkon kama aikinsa.

Manchester United tana matsayi na shida a teburin firimiya lig mako na 22 da maki 41, dai dai da Arsenal wadda take mataki na biyar ita ma da maki 41, ban bancin kwallaye biyu tsakaninsu.