Ba Mamaki Dan Wasa Neymar Ya Tsallake Da Baya!

An dakatar da hukuncin haramta wa dan wasan PSG Neymar buga wasanni uku.

Kotun sauraron kararrakin wasanni (Court of Arbitration) ta janye dakatarwa guda daya daga cikin uku da aka yi wa dan wasan gaban Paris St-Germain Neymar.

Hukumar da take shirya gasar Zakarun Turai ce dai ta dakatar da Neymar buga wasanni uku, sakamakon cin zarafin wasu alkalan wasa da yayi a bayan kungiyar Manchester United, tayi waje rot da Paris-saint German a gasar cin kofin zakarun turai UEFA Champions League 2018/19, da kwallaye 3-1 ranar 6 ga watan Maris 2019.

Dan wasan Neymar mai shekaru 27 da haihuwa ya ai yana bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka ba Manchester Unitet a na daf a tashi a matsayin haramtacciya ce, kuma abin kunya ne ga Alkalan wasan da ya hura.

Sai dai Neymar bai buga dukkannin wasanni biyu da PSG ta kara da Manchester ba, sakamakon rauni da yayi a yatsun kafarsa.

A kan hakane hukumar UEFA tace ya karya doka da irin wannan kalamai, ta kuma dauki matakin ladab tarwa kan dan wasan.

Matakin da hukumar ta UEFA ta dauka ya sanya Neymar ba zai buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Real Madrid da Galatasaray ba.

Sai dai zai taka-leda a ranar 22 ga watan Oktoba a wasan su da Club Brugge a Champions League.