Ba Makawa Ghana Zata Shiga Gasar Kwallon Olympic-Tanko

Ibrahim Tanko

Mai horar da kungiyar ‘yan wasan Ghana ‘yan kasa da shekaru 23 ta Black Meteors, Ibrahim Tanko, ya lashi takobi cewa zai tabbatar da ganin Ghana tayi fice a rukunin A a gasar Africa kafin zuwa Olympics a shekarar 2020 a birnin Tokyo na kasar Japan, dauk da cewar abokan karawarsa na barazana.

Black Meteors tana tare da Misra mai masaukin baki, a cikin rukunin A tare da Kamaru da Mali, a gasar zakarun Afrika ‘yan kasa da shekaru 23 a Misra, inda kungiyoyi uku da da zasu yi fice a wannan gasar zasu samu cancantar shiga babbar gasar ta Olympic a Tokyo.

Tanko da ya halarci taron karkasa kungiyoyin wasan, yace Ghana ta fada a cikin rukunin mai karfi, amma duk da haka zata yi fice a wannan rukunin. Yace shi kansa yafi son irin wannan rukuni mai karfi fiye da rukunin da ake cewa mara karfi.

Idan mutum ya samu kansa cikin irin wannan rukuni kaima ka san akwai aiki sosai a gabanka, a don haka zaka yi duk iya bakin kokarinka kayi nasara saboda ka san babu kungiya mai sauki.

Ibrahim Tanko yace a cikin kowace gasa, wasan farko yafi muhimmanci kuma Ghana zata yi wasanta na farko ne da kasar Kamaru kuma ya kyautata zaton zai yi nasara.