Ba Jihohi Izinin Kafa Nasu 'Yansandan Bai Dace Ba Yanzu-Tsav

IBRAHIM K. IDRIS, babban sifeton 'yansandan Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta soma yin wani muhawara akan baiwa jihohi izinin kafa nasu rundunar 'yansanda wai domin samun cikakkiyar dimokradiya

Sabili da wannan muhawarar da majalisar wakilai ta soma ya sa Muryar Amurka ta zanta da tsohon kwamishanan 'yansanda Alhaji Abubakar Tsav yayi bahasi akai.

Alhaji Tsav yace dimokradiyar Najeriya bata kai inda za'a ba jihohi izinin kafa nasu rundunar 'yansandan ba domin akwai wasu gwamnoni masu ikon gaske da zasu saka 'yansandan cikin aljuhunsu. Yin hakan zai dada raba kasar.

Lokacin da ake da 'yansandan yankuna a kasar an sha kone mutane saboda 'yansandan sun samu umurni daga shugaban yankin kuma babu abun da zasu yi. Ya tuna da lokacin da aka samu rigima a kasar. 'Yansandan dake yankin gabashin kasar sun zama 'yan amshin shatan Ojukwu. Sai abun da yace su keyi.

Yace idan al'ummar kasar ta waye sosai to ana iya ba jihohi izinin kafa nasu 'yansandan amma ba yanzu ba. Idan an yi haka yanzu masu iko zasu bata kasar. Idan ma an zo daukan 'yansandan gwamnoni zasu cikasu da 'yan bangan siyasarsu lamarin da zai kara dagula abubuwa.

Dangane da cin hanci da rashawa Alhaji Tsav yace abun ma zai fi muni da 'yansandan jihohi.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Jihohi Izinin Kafa Nasu 'Yansandan Bai Dace Ba Yanzu-Tsav - 3' 00"