Ba Alamar Wani Sabani Tsakanin Shugaba Buhari Da Tsohon Shugaba Obasanjo.

  • Ladan Ayawa

Buhari da Obasanjo

Ganawar da Shugaba Buhari yayi a bainar jamaa shida tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta nuna cewa suna siyasa bada gaba ba.

Gaisawar da shugaba Muhammadu Buhari yayi da tsohon shugaban Olusegun Obasanjo a taron Kungiyar Tarayyar Africa, a Addis Ababa ta nuna cewa wani darasi ne ga ‘yan siyasa.

Idan dai ba a manta ba, a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ne tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya rubutawa Shugaba Muhammadu Buhari wasika yana caccakarsa da gwamnatinsa.

A cikin wasikar ma har ya shawarce shi da kar ya tsaya takara a zabe mai zuwa, abinda ya janyo muhawara a cikin kasa tsakanin rukunin mutane daban-daban.

Sai dai mai Magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, wato Mallam Garba Shehu yace tsohon shugaba Obasanjo ba ya wakiltar ra'ayin dukkan ‘yan Najeriya.

Ga Nasir Adamu El-Hikaya da Karin bayani.2’44

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Alamar Wani Sabani Tsakanin Shugaba Buhari Da Tsohon Shugaba Obasanjo.