Bayan da kungiyar kwallon kafa na Manchester United ta sallame shi daga aikin horas da 'yan wasanta a 2018, cikin watan Disamba kimanin shekara biyu Jose Mourinho, na bukatar ganin ya koma kasar Ingila domin jan ragamar horaswa.
Mourinho yace yana sha'awar komawa Ingila ne, saboda sha'awar lashe manyan kofuna tare da kungiyoyi uku na firimiya.
Tsohon kocin mai shekaru 56 da haihuwa wanda yanzu haka yake zaune a gidansa dake Burtaniya, ya ki karbar aiki da wasu kungiyoyi kwallon kafa na kasashen duniya suka masa, ciki harda kulob din Benfica da kuma tayin kwantirakin Fam miliyan £88m, da wata kungiya ta kasar Sin tayi masa.
Mourinho ya koma Sky Sports a matsayin mai sharhi kan wasanni tare da Roy Keane, Gary Neville, Graeme Souness sai Jamie Redknapp.
Sai dai wasu rahotanni na cewar da yuwar Jose Mourinho ya maye gurbin kocin Real Madrid Zinedine Zidane, wanda ake ganin kulob din na iya sallamarsa, saboda rashin tabuka abun kirki a kakar wasan bana.
A shekaru biyu da ya yi a Manchester United, Mourinho ya lashe kofin
Europa League, da kuma Community Shield na Ingila kafin daga bisani Ole Gunnar Solskjaer ya maye gurbinsa.