Rahotanni daga jihar Taraba na cewa akwai wasu yankuna na kudancin jihar da ba a gudanar da zabe ba, lamarin da ya tada hankulan al’ummomin da abin ya shafa.
Kamar yadda al’ummar wasu yankunan kananan hukumomin Wukari da Takum dake zama mahaifar gwamnan jihar Taraban ke cewa, kawo zuwa cikin dare akwai wasu wuraren da ba’a gudanar da zaben ba, lamarin da al’ummun ke dangantawa da yunkurin magudin zabe.
Yankin Chinkai na Wukari na cikin wuraren da ba’a yi zabe ba, kuma kawo yanzu suka ce basu san makomarsu ba, gama dai ta bakin wani mazaunin garin.
Cikin garin Wukari ma dai an dan samu hatsaniya kan matsugunin wani akwati, lamarin da ya kai jami’an tsaro dauke akwatin zuwa ofishin 'yan sanda, kamar yadda wannan mazaunin garin Wukarin yayi Karin haske.
Na dai ta kokarin ji daga bakin kwamishinan hukumar zabe ta INEC a jihar kan wadannan matsaloli, to amma haka ta bata cimma ruwa ba, koda yake daya daga cikin jami’an dake hulda da jama’a a hukumar Mr Marvin Mathias, yace suna sane da batun na cikin garin Wukarin, amma zasu bincika game da na sauran yankunan.
Ya dai zuwa lokacin hada wannan rahoto gwamnan jihar Taraba Akitet Darius Dickson Isiyaku, shi da wasu jami’an gwamnatin jihar duk sun tare a Takum game da wannan zabe, ya yin da tuni aka soma hada hancin sakamakon zaben wasu yankuna.
Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’Aziz.
Your browser doesn’t support HTML5