An tura karin jami’an tsaro zuwa jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, domin ganin an gudanar da zaben gwamnan da ake yi yau cikin kwanciyar hankali.
Wannan kuma na zuwa ne yayin da hukumar zabe INEC, ke musanta rahotanin cewa an sake dage zaben, batun da ta ce ba haka lamarin yake ba.
Kwamishinan hukumar zaben ta INEC a jihar Adamawan Barr. Kassim Gana Gaidam, ya ce za’a gudanar da zaben ne a rumfuna 44 a kananan hukumomi 14 na jihar Adamawan.
Kawo yanzu tuni karin jami’an tsaron da aka turo domin wannan zaben suka isa da suka hada da 'yan sandan kwantar da tarzoma da jami’an tsaron farin kaya na DSS, da aka turo daga wasu jihohi domin sa ido.
Tuni sabon kwamishinan rundunan 'yan sanda a jihar A.A Madaki ya tabbatar da cewa za su kare rayuka da kuma dukiyoyin jama'a.
Za’a dai gudanar da zaben ne, yayin da ake sa ran a gobe Jumma’a za’a yanke hukunci a shari’ar da jam’iyar MRDD ta shigar gaban wata kotun ta jihar Adamawan bisa zargin cewa ba’a saka tambari ko alamar jam’iyyar ba watau logo, a takardar kada kuri’a.
Ita dai hukumar zaben ta ce jam’iyyar ba ta cika ka’idojin tsayar da dan takara ba.
Saurari cikakken rahoton Ibahim Abdulaziz daag Yola:
Your browser doesn’t support HTML5