Lamuran ayyukan gwamnati sun tsaya cik a jihar Zamfara sakamakon yajin aikin na sai baba ta gani da hadakar kungoyin kwadagon jihar suka shiga.
Kungiyar kwadagon ta soma yajin aikin ne da safiyar yau bayan ta kammala wani taronta a daren jiya. Ta umurci duk ma'aikatan gwamnati kada su fito aiki. Haka kuma ta bukaci kasuwanni da tasoshin motoci kada su bude wuraren kasuwancinsu.
Bashir Muhammad Mafara shugaban kungiyar kwadagon jihar Zamfara ya bayyana dalilansu na shiga yajin aikin. Ya na mai cewa akwai matsala da biyan albashi mafi kankanci na Nera dubu goma sha takwas wanda ya zama dokar kasa. A cewarsa a jihar Zamfara suna da ma'aikatan da ko dubu goma ma ba'a biyansu.
Matsala ta biyu ita ce rashin biyan kudin karin girma da ake yiwa ma'aikata na tsawon shekaru da dama. Baicin hakan akwai masu jiran kudin sallamar wadanda suka bar aiki bayan sun yi shekaru 35 suna aikin. Wadannan kudaden sun lake basu samu ba. Malam Basir yace duk yunkurin da suka sha yi domin a samu a biyasu, hakansu bai kai ga cimma ruwa ba.
Ya ambato wasu matsaloli bakwai da ya ce sun rubuta a takardar da suka ba gwamnati tare da ba da wa'adin kwani 21 a biya masu bukatunsu. Jiya wa'adin ya cika kuma gwamnati bata ce masu komi ba. Dalili ke nan suka shiga yajin aiki na sai abun da hali ya yi.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5