A halin da ake ciki, kasar Australia ta ce dukkan matafiya zuwa kasar su kebe kansu na kwanaki 14 kuma babu wani jirgin ruwan da zai shigo tashar kasar.
Firai ministan kasar Scott Morrison ya fada a jiya Lahadi cewa an dauki wadannan matakan ne domin dakile yaduwar cutar coronavirus a kasar ta Australia.
Ya cigaba da cewa, "za mu wajabta amfani da matakin kariya da duniya ta ayyana na kebe-kai, ga duk wadanda suka shigo kasar, farawa daga daren yau. Bugu da kari, gwamnatin Australia ta hana jiragen ruwa shigowa kasar cikin kwanaki 30."
Kasar Sipaniya kuma ta sanar ranar Asabar cewa zata yi matukar takaita tafiye tafiye a cikin kasar mai dauke da mutum miliyan 46 domin dakile yaduwar cutar ta coronavirus da ta zamo annoba a nahiyar Turai.
Firai Ministan kasar Pedro Sanchez ya kara da cewa, “ina so na isar muku da wannan sakon na cewa burinmu da kuma aniyarmu sun kai matuka. Wadannan matakai na kare ‘yan kasa ne da kuma dakile kwayar cutar. Sannan daga yanzu za mu shiga wani sabon babi inda za mu yi amfani da wasu tanaje-tanajen doka da kundin tsarin mulkin kasa ya amince da su a lokacin annoba.”