Australia Ta Cimma Matsaya Ta Sayan Miliyoyin Rigakafin COVID-19

Wani samfurin riga-kafin na Covid-19

Kasar Australia ta cimma wata matsaya ta sayen rigakafin cutar COVID-19 har miliyan 25.

Ta cimma matsayar ne da wani kamfanin hada magunguna da ake kira AstraZeneca na Birtaniya, rigakafin da a halin yanzu ke mataki na karshe-karshe na gwajinsa da ake yi a jikin bil adama.

A jami’ar Oxford ta Birtaniya aka samar da rigakafin aka kuma ba kamfanin hada magungunan lasisin yin amfani da shi, wanda aka yi masa lakabi da AZD 1222.

Frai ministan Australia, Scott Morrison

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Firai Ministan Australia, Scott Morrison, ya ce rigakafin na jami’ar Oxford, na kan gaba cikin wadanda ake sa ran za su yi aiki cikin jerin gwaje-gwajen da ake yi a sassan duniya.

Ya kuma kara da cewa, ana sa ran nan da shekara mai zuwa, za a raba maganin kyauta ga kowanne dan kasra ta Australia.