Australia ta bayarda sanarwar a yau Talata cewar zata dakatar da hare-haren da mayakanta na sama suke kaiwa a tsakiyar Syria na wani lokaci.
Wannan matakin yana zuwa kwanaki kadan a bayan da wani jirgin saman yakin Amurka ya harbo wani jirgin saman yakin Syria, abinda ya sa kawar Syria din, watau Rasha, tace daga yanzu zata dauki duk wani jirgin saman yaki na kasashen kawancenda Amurka take jagoranta a zaman na abokan gaba a samaniyar Syria.
Australia tana cikin kasashen kawancen da suka fara kai hare-hare daga sama a kan mayakan Daesh ko ISIS cikin kasar Syria a watan Satumbar 2014.
Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron Australia ta ce zata nazarci yanayin samaniyar Syria ta kuma yanke shawara a kan abinda zata yi nan gaba. Australia ta ce zata ci gaba da kai hare-hare ta sama a makwafciyar Syria, Iraq.
Jiya Litinin Amurka ta mayarda martini da kakkausan harshe ga wannan barazana ta Rasha.