An kama Wa Lone da Kyaw Soe Oo tun a watan Disamban bara bayan ganawarsu da wasu jami'an 'yan sanda biyu a wani wurin cin abinci a Yangon inda aka ba su wasu kundin bayanai. Su na binciken kashe wasu Musulmin 'yan kabilar Rohingya su 10 da 'yan sanda da soja su ka yi a kauyen Inn Din bara. An yanke ma 'yan jaridan biyu hukuncin daurin shekaru 7.
Da ta ke magana a babban taron kasa da kasa kan tattalin arziki wanda ake yi a Hanoi, babban birnin kasar Vietnam, Aung San Suu Kyi ta yi kira ga duk wanda ya soki lamirin hukuncin tare da kiran a saki 'yan jaridar, ciki har da Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence, da ya fito fili a bayyana inda aka yi rashin adalci a shari'ar.
Kungiyar kare hakkin Bil'Adama ta kasa da kasa Amnesty International, ta soki Aung San Suu Kyi saboda kare gwamnati kan hukuncin da aka yankewa 'yan Jaridar.