Atiku Ya Kai Gangamin Yakin Neman Zabensa Jigawa

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyar PDP Atiku Abubakar a Jigawa (Hoto shafin Twitter Atiku)

Gangamin yakin neman zaben tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa karkashin babbar jam’iyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya kai ziyara a jihar Jigawa.

‘Yan takara a matakai daban-daban na ta yakin neman zabe a sassan kasar yayin da aka tunkari zabe a watan gobe.

Tshohon mataimakain shugaban kasar na Najeriya ya garzaya shafinsa na Twitter yana mai nuna godiyarsa ga jama’ar Jigawa bayan da aka kammala gangamin.

“Na Gode Jigawa.” Atiku ya rubuta.

Ziyarar ta Atiku Abubakar a jihar ta Jigawa, na zuwa ne kwanakin kadan bayan takaddamar ficewar da dan takarar na PDP ya yi a zauren muhawara a ranar Asabar, yana mai cewa ya dauki matakin ne saboda shugaba Buhari bai bayyana ba.

Yayin da wasu ke sukar wannan mataki wasu kuwa yabawa suka yi.

Kai gangamin yakin neman zaben nasa zuwa Jigawa har ila yau, na zuwa ne kwanakin kadan bayan da ya dawo daga wata ziyarar kwanaki biyu da ya kai Amurka wacce ita ma ta kasance mai cike da takaddama.