A Kalla Mutane 347 Sun Hallaka a Kasar Cambodia

  • Ibrahim Garba

Wasu daga cikin wadanda turereniyar ta rutsa da su kenan a ke zuba su cikin mota a-kori-kura

A kalla mutane 347 sun hallaka daruruwa kuma sun raunana a Cambodia

A Kalla Mutane 347 Sun Hallaka Daruruwa Kuma Sun Raunana a Wata Turereniya a Wani Babban Buki a Phnom Penh, Babban Birnin Kasar Cambodia.

Hukumomi sun ce galibin wadanda abin ya rutsa da su au an tattake su ne au sun shake lokacin da cincirindon jama’a a tsibirin kogin Tonle Sap su ka firgita su ka zabura don ketare wata gada.

Shaidun gani da ido sun ce wasu mutanen ruwa ne ya ci su bayan sun rikito daga kan gadar zuwa cikin kogin.

Da ya ke magana da safiyar yau Talata,Firayim Ministan Cambodia Hun Sen ya bayyana turereniyar da cewa ita ce bala’I mafi munin day a taba abka wa kasar tun bayan gwamnatin Kwaminisancin Khmer Rouge da ta yi mulkin kama karya a 1970. Ya bayar da umurnin a yi bincike ya kuma aje ranar Alhamis a matsayin ranar makoki a kasar baki daya.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta aike da sakon ta’aziyya a madadin Amurka saboda rayukan da aka yi asararsu ta kuma ce ta na da kwarin gwiwar cewa mutanen Cambodia za su rungumi kaddara a wannan mawuyacin lokacin.