Asusun tallafawa yaki da cututuka na duniya-Global Fund ya bada tallafin dala miliyan biyu da dubu dari biyar domin yaki da cutar kanjamau a jihohi goma sha biyu na Najeriya da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Asusun ya bada tallafin ne musamman domin ceton rayukan jarirai ta wajen hana yada cutar daga uwa zuwa jariri.
Bincike na nuni da cewa, kashi saba’in cikin dari na jarirai sama da dubu biyu da aka Haifa da kwayar cutar kanjamau daga Najeriya suke. Abinda ke nuni da cewa mata masu ciki dake dauke da cutar kanjamau basu samun magani da suke bukata.
Darekta janar na hukumar yaki da cutar kanjamau a Najeriya Farfesa John Idoko yace kashi talatin bisa dari na matsalar yaki da cutar kanjamau yana Najeriya, yace kasashe da suka ci gaba sun daina samun jarirai da suke daukar cutar kanjamau daga iyayensu amma har yanzu ana fama da matsalar a Najeriya.