Asusun Tallafa wa Yara Na Majalisar Dinkin Duniya Ya Tura Tallafin Kayan Masarufi Ga Yan Gudun Hijirar Myanmar Da Ke Bangladesh

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutarres

Asusun tallafa wa Yara Kanana na Majalisar Dinkin Duniya da ake kira UNICEF a takaice ya fada a yau Alhamis cewa, manyan motoci dauke da kayan agaji ga yaran da rikicin gudun hijirar Rohingya ya shafa na kan hanyar su zuwa Bangladesh, inda daruruwan al’ummar Rohingya ta Myanmar suka gudu domin tsira da rayuwarsu.

Kamar yadda Asusun Kula Da Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai fiye da 'yan Rohingya 400,000 da suka gudu daga Myanmar zuwa Bangladesh, haka kuma kaso 60 cikin dari yara ne kanana.

Daga cikin taimakon kayan da Hukumar Kula da Yaran ta Majalisar Dinkin Duniya ta aika da su akwai Ruwa, da kayan tsaftace muhalli, da sutura da kuma sauran kayan da ake bukata, Hukumar ta ce ta shirya aikawa da wasu kayayyakin cikin makonni masu zuwa.

An bada sanarwar agajin ne bayan Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana al’amarin da kisan kare dangi.