"Kama daga jami'an mu da ke kan tituna, zuwa masu aiki a bangaren ba da lasisi da sauran su, za su samu damar shiga manhajar don kwarmaton cin hanci" Inji shugaban hukumar kiyaye aukuwar haddura ta Najeriya (Roadsafety), Boboye Oyeyemi, a taron kaddamar da manhajar ba da labaru don yaki da cin hanci da asusun AKIN FADEYI da MACARTHUR su ka dauki nauyi a Abuja.
Oyeyemi wanda hukumar sa ce ta farko da ta amince da shiga manhajar, ya ce, ta hanyar kwarmaton za a samu ladabtar da masu laifi da kuma ba da lada wadanda su ka yi aiki mai kyau.
Manhajar dai da mutum zai iya sauketa kan wayar sa ta salula, za ta zama hanyar ba da labari cikin sauri don dakile zarmiya ba tare da ma baiyana sunan wanda ya kwarmata labarin ba.
Simon Adole John, jami'in asusun AKIN FADEYI da MACARTHUR, ya ce, duk 'yan Najeriya ka iya amfani da manhajar mai suna FLAG'IT.
Gwamnatin Najeriya ta bakin shugaban hukumar wayar da kan jama'a Dr. Garba Abari, ya ce, wannan manhaja sara ne kan gaba.
Wannan dandali dai ba kamar na kwarmaton da gwamnatin ke alwashin ba da ladar kashi 5% na adadin kudi ga wadanda su ka samo labari ba ne, wanda kalubalen sa ya jefa aiki da rayuwar 'yan Najeriya da dama cikin garari, ba lada ba la'ada sai gararamba wajen lauyoyi da buga takardu barkatai.
Labarun da mu ke samu na nuna mutane da dama sun daina zumudin ba da labarun zarmiya don gudun shiga rudani.
Ga cikakken rahoton Wakilin Muryar Amurka daga Abuja, Nasiru Adamu El-hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5