Assad ya Nuna Damuwa ga Cijewar Shirin Zaman Lafiyar Syria

Bashar Assad-Shugaban Syria

Bashar Assad-Shugaban Syria

Shugaban kasar Syria Bashar Assad ya bayyana nadamarsa ga cijewar shirin shiga tsakanin bangarorin adawar Syria a Geneva da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a makon da ya gabata.

Sai dai shugaban na Syria ya kyautata zaton samun kyakkyawar sakamako a tattaunawar zaman lafiya da za a yi cikin watan Faburairu 2018 a birnin Sochi da Rasha zata dauki nauyi.

Wadanda ake tattaunawa dasu a Geneva, yan adawan Syria basu wakiltan mutanen Syria kuma an yi wannan tattaunawa har na tsawon shekaru uku, amma babu wata nasara da Geneva tayi, Assad ya fadawa maname labarai a safiyar jiya Litinin a birnin Damascus, sai dai yana zaton a kwai rawar da MDD zata iya takawa a nan gaba a shirin zaman lafiyar Syria.

Shirin tattaunawar zaman lafiya tsakanin bangarorin Syria tayi zama sau takwas a Geneva amma babu wata nasarar kirki da aka samu. Wannan ne kuma ya yi dalilin wata tattaunawa a wanannan mako a birnin New York tsakanin manzon MDD na musamman a Syria Staffan de Mistura da sakataren MDD Antonio Gutteres da kuma kwamitin sulhun MDD.