Asisat Oshoala Ta Taimakawa Barcelona Kaiwa Ga Nasara

'Yar wasa Asisat Oshoala ta zura kwallaye biyu da su ka taimakawa Barcelona lashe kofin zakararu a bangaren mata na Spanish Super Cup bayan ta doke kungiyar Real Sociedad da ci 10-1 ranar Lahadi.

Wannan ita ce nasarar farko da kungiyar ta samu a wannan kakar, kuma kwallayen da matashiyar mai shekaru 25 ta zura, sun karawa wasan armashi da kuma bada kwarin gwiwa ga nasarar kungiyar.

Asisat ce 'yar wasan kwallon kafar Afirka ta farko a tarihi da ta lashe wannan kambin tun bayan da ta fara bugawa kungiyar wasa a shekarar 2019, inda ta zura kwallaye 19 cikin wasanni 22 a wasannin gasar bana.