WASHINGTON, DC —
'Yan Tawayen Mali akasari Asbinawa, sun rattaba hannu kan yarjajjeniyar zaman lafiya da gwamnatin Mali, sama da wata guda bayan da wasu kungiyoyin mayaka su ma su ka dau wannan matakin, don kawo karshen tashe-tahsen hankula a wannan matalauyar kasar hamada da yaki ya daidaita.
Wannan yarjajjeniya, wadda MDD ta taimaka aka cimma, ta tanaji gudanar da zaben Majalisun Dokokin larduna a Mali, to amma saura kiris ta ba da 'yancin cin gashin kai ga arewacin Mali, wanda akasarinsa ke cikin hamadar Sahara. Bukatar 'yan awaren ita da babbar sanadin boren da ya kai ga juyin mulkin soji, wanda ya yi sanadin hambare Shugaban Mali, wanda ya fito daga yankin da ke kudu da Saharar.