Arsene Wenger ya fara zawarcin dan wasan nan Pierre- Emerick, a halin da ake ciki yanzu kulob din na Gunners shine kan gaba a wasannin premier league, inda suka wuce Leicester da maki biyu, Manchester City kuma da maki uku.
Borussia Dortmund na matukar ra’ayin cigaba da rike dan wasan gaban na su wanda ya jefa kwallaye har sau 27 a wasanni 27 a wasannin da aka buga na kakar bana, dan haka a shirye suke domin kin amincewa da zawarcin dan wasan da Arsenal ke yi.
A cewar mujallar The Sun, a shirye Wenger yake ya zuba zunzurutun kudi har fan miliyan 42 domin sayen dan wasan, kuma ana kyautata zaton ya riga ya fara Magana da kulob din.
Shugaban wucin gadin kulob din na Chelsea Guus Hiddink ya nuna matukar farin cikinsa ga John Mikel Obi bayan bajintar da dan wasan ya nuna yayin da kulob din ya doke Crystal Palace da ci 3-0 a fafatawar da suka yi jiya lahadi.
Dan wasan asalin dan Najeriya ya fara taka leda ne a lokaci daya da Cesc Fabrigas inda ya taka rawar gani musamman wajan nasarorin da kulob din ya samu.
Hiddink ya nuna maukar farin ciki da godiya ga Mikel Obi innda yace dan wasan ya yi wasa mai ban shi’awa kwarai a wasan dama sauran wasannin da suka gabata.