Arsenal: Zamu Sayi Dan Wasa Nicolas Pepe A Kakar Bana

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Thierry Henry, ya bayyana cewa babban kuskure ne ga Arsenal, idan har suka yarda suka kashe makudan kudade wajen sayan dan wasa Nicolas Pepe, inda ake rade radin yana dab da komawa kungiyar a kakar wasa mai kamawa.

Henry yace babban kuskure ne kashe irin wannan kudaden akan dan wasa guda daya, kuma bashi ne matsalar kungiyra Arsenal ba.

Inda yace kungiyar a yanzu tana bukatar ‘yan wasan baya manya, kamar
guda biyu ne domin tun karar wasan mai zuwa na 2019/20.

Arsenal dai ta cimma yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Lille, dake kasar Faransa domin sayen dan wasan gefen na Ivory Coast Nicolas Pepe, kan zunzurutun kudi har fam miliyan £72, kuma Arsenal din za su biya kudin a hankali domin ya yi dai-dai da karfin aljihunsu.