Arsen Wenger Ya Mayar Da Martanin Sukar Da Akayi Masa

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger yace ana wuce gona da iri a sukar da ake yi ma kungiyar kan yadda take kokari, ko rashinsa, na lashe gasar lig na firimiya na Ingila a bana.

Dukar da Arsenal ta sha kashi a hannun Manchester United da ci 3-2, duk da cewa ‘yan wasan United da dama sun ji rauni basu buga wasan ba, ya sanya yanzu Arsenal tana bayan Leicester City da maki 5 a saman firimiya Lig, abinda zai kara mata shakku a yunkurin kawo karshen rashin wannan kofi na tsawon shekaru 12.

‘Yan fashin baki a kafofin yada labarai sun dira a kan Arsenal bayan wannan wasa, inda tsohon manajan Liverpool, Graeme Souness yace basu da kuzari ko alamarsa, wani tsohon dan wasan Arsenal din kuma, Paul Merson, yace ya kamata Wenger ya sauka daga kan kujerarsa ta manaja idan har Arsenal ba ta lashe Firimiya Lig bana ba.

Wenger ya fadawa taron ‘yan jarida kafin wasan da Arsenal zata yi yau da Swansea City cewa shi kam bai yi mamaki da irin sukar da ake yi ba. Yace haka kafofin yada labarai suke a yanzu. Wani bangare na wannan sukar ya wuce gona da iri, amma tilas mu ji shi.

Wenger yace mutane suna mayar da martani ko yin sharhi cikin fushi ko yayin da hankulansu ya tashi, amma su abinda zasu yi shine su zauna cikin tsanaki suyi nazarin wannan lamarin. Yace ana mutunta Arsenal a duk fadin duniya duk da abubuwan da mutane suke fada. Kowa na da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa, kuma ina jin dadin cewa akwai wadanda suka damu kan makoma ta.

A karshen mako, Arsenal zata kara da kungiyar Tottenham Hotspur wadda take ta biyu a teburin Firimiya Lig, kuma Wenger yana son wasan da zasu yi da Swansea City a yau laraba ya zamo matakin farko a yunkurin Arsenal na hayewa zuwa saman teburin na Firimiya Lig.