Arjen Robben Bazai Taka Leda Na Tsawon Makonni Shidda Ba

A daidai lokacin da kulob kulob na nahiyar Turai suke shirye shiryen tunkarar sabuwar kakar wasanni shahararren dan wasan Beyern Munich ta kasar Jamus Arjen Robben bazai taka led aba har na tsawon makonni shidda sakamakon rauni da yake fama da shi.

Robben dan shekaru 32 bai buga wasa a watanni biyu na karshen kakar data gabata sakamakon irin wannan raunin amma ya buga wasan shirye shiryen sabuwar kakar wasanni da kungiyar ta buga da kungiyar kwallon kafa ta livestart inda raunin nasa ya sake komawa danye, sau goma sha biyar ne kacal ya buga wasannin a kakar wasannin kakar data wuce.

Wata mai kama da wannan kuma itace tsohon dan wasan Chelsea Demba Ba, shima yana fama da raunin da ake fargaban cewa zai iya kawo karshen wasa a gare shi sakamakon karya kafa da yayi sa’adda yake wasa a gasar super league ta kasar China.

Ba dan kasar Senegal mai shekaru 31, ya fadi ne sa’adda yayi karo da wani dan wasa inda ya karya kafarsa ta hagu, lamarin ya auku ne sa’adda yake bugawa kulob dinsa na kasar Sin wasa, wanda ya nkoma a watan Yulin daya gabata akan kwantaragin kudi Euro miliyan 12, bayan da ya baro kungiyar kwallon kafa ta kasar Turkiyya.

Kafin aukuwar lamarin Demba Ba, shine ke kan gaba wajan fin kowa zura kwallaye a gasar inda yake da kwallaye 14, a cikin wasannin 18.

A bangare daya kuma tsohuwar kungiyar Demba Ba, wato Chelsea ta rattaba hannu da dan wasan zakarun Premier wato Leister City N’Golo Kante, a kwanatarin shekaru 5, da aka bada tabbacin kudin su zai kai Euro miliyan 30. Kante na cikin ‘yan wasan kasar Faransa da suka kai karshe a wasan gasar cin kofin Turai na wannan shekara wacce aka kammala.