Gamaiyar kungiyoyin arewacin Najeriya CNG ta ce yankin arewa na da dimbin hanyoyin tara haraji da za su cike gurbin kudurin dokar sabunta haraji da ke gaban majalisar dattawa.
Wannan ya biyo bayan zama da kwararru kan hanyoyin raya tattalin arziki da kungiyar ta yi a Abuja don neman mafita idan kudurin ya samu nasara.
CNG wacce ta sake nanata bukatar dakatar da kudurin don yi ma sa garambawul da zai dace da muradun kowane yanki, ta ce hakki ya rataya a kan ‘yan Arewa a majalisa su tabbatar ba a yi wa yankin sakiyar da ba ruwa ba.
Shugaban gamaiyar kungiyoyin Jamilu Aliyu Charanci ya ce arewa ka iya samun dimbin kudin shiga daga albarkatun noma da kiwo muddin “an tabbatar ana karbar haraji kan duk buhun abinci da za a fitar daga arewa a kuma daina kai shanu kai tsaye kudu maimakon haka a rika yankawa a na tura naman”.
Wannan matsaya ta zo daidai da hangen tsohon sakataren gwamnati Mr.Babachir David Lawan wanda ya yi misali da arzikin noma da kiwo na jihar Adamawa “an tare ka an kirga shanu a ka ce kowace saniya ka biya haraji Naira dubu biyar, na yi lissafi a shekara ba za mu gaza samun akalla Naira biliyan kusan dari ba. A na zuwa Mubi a na sayan shanu 300,000-400,000 to in ka kara N5000 a kai ya yi wani abu ne?”
Jamilu Charanci ya yi hannunka mai sanda ga ‘yan majalisar “al’umma su tashi su rike ‘yan majalisar su gam, wannan kudurin idan ya tsallake ba wadanda su ka cuce mu sai ‘yan majalisar mu, idan kuma a ka maido shi a ka janye shi to ku sani ba wanda ya taimake mu sai ‘yan majalisar mu”
Domin sauraron rahoton cikaken rahoton Nasiru, a latsa nan: