AREWA A YAU: Batun Yada Jita-Jita Ko Farfagandar Karya, Satumba 7, 2022

Nasiru Adamu El Hikaya

Shirin wannan makon ya tabo batun illar yada jita-jita ko farfagandar karya ta hanyar daukar hirar wasu kamar ta zancen wayar tarho don isar da wasu sakonni da za a yi tsammani na sirri ne alhali duk shiri ne na muzanta wasu abokan hamayya.

ABUJA, NIGERIA - Masu wannan dabi’a ba sa ambata sunansu kuma ba sa nuna hotunansu, sai su yi doguwar hira amma tamkar ta hanyar cin amana aka nadi hirar a faifai.

Masu mummunar dabi’ar kan fi yin amfani da yanar WHATSAPP wajen yada farfagandar ga jihohin arewa 19.

Bayan haka shirin ya tabo yadda ‘yan arewa za su iya sauya yankin zuwa mai tsaro da arziki kamar a baya ta hanyar samun jagoranci nagari.

Dr. Muhammad Bashir Sa’idu da Abdullahi Manaja Bauchi sun bada gudunmawa a shirin.

Saurari cikakken shirin Nasiru Adamu Elhikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU: Batun Yada Jita-Jita Ko Farfagandar Karya