Apple Ta Sauke Manhajar Dake Jefa ‘Yan Sandan Hong Kong Cikin Hadari

Wayar Apple

Wayar Apple ta sauke manhajar taswira da ake kira “Real-Time Mapping App” mallakar ma’aikatar gudanar da taswira kai tsaye ta Hong Kong da masu zanga zanga a Hong Kong suka yi amfani da shi domin gano inda ‘yan sanda suke.

Apple tace ta janye wannan manhaja ce saboda kararraki da ake kawo mata game da manhajar, haka zalika tace amfani da manhajar yana jefa rayuwar jami’an tsaro da mazauna Hong Kong cikin hadari.

Wannan manhajar tana nuna inda ‘yan sanda da kuma hukumomin Hong Kong suka tabbatar da haka kuma ana amfani da ita a auna ‘yan sanda har ma akai musu harin kwantar bauna, inji Apple a hira da tayi da manema labarai.

Apple tace wannan manhaja ta sabawa sharudodin Apple da ma dokokin cikin gida a don haka ne muka janyeta daga dandalin sukae manhajojinmu.

Ma’aikatar gudanar da taswira kai tsaye ta Hong Kong (HKmap) ta maida martani da kakkausar lafazi a wani sakon Twitter, tana kwatanta wannan mataki da harkar siyasa. HKmap tace bata gamsu da abin da Apple ke fad aba cewa manhajarta tana jefa rayuwar ‘yan sanda da mazauna Hong Kong cikin hadari ba,

Tace galibi masu amfani da manhajar ne ke zuba abubuwa dake ciki inji HKmap, ta kuma kara da cewa a matsayinta na mai gudanar da manhajar, tana iya bakin kokarinta ta fitar da duk wasu abubuwa da ka iya janyo miyagun ayyuka a kan manhajar.