Apple Da Google Za Su Fitar Da Sabbin Alamun Emojis

Kamfanonin Apple da Google na shirin fitar da wasu sabbin manuniya ta ‘Emojis’ wadanda akan yi amfani da su wajen bayyanar da wasu kalamai batare da rubutu ba, ko dai mutum ya nuna halin da yake ciki ko wani abu makamancin hakan.

A jiya ne dai aka yi wannan ranar ta Emoji ta duniya, wanda kamfanonin ke ayyana cewar kara yawan wadannan alamomin zai taimaka wajen hada kan jama’a, don kada wasu mutane ko wasu nau’ukan abubuwan rayuwa suga kamar an nuna musu wariya.

Wasu daga cikin sabbin alamun sun hada da nau’in jinsin fata, sai wanda ke nuna alamun nakasassu, da na wanda aka yanke ma kafa, haka akwai na Kare mai yima mutane jagora, kana akwai na kurame wanda zai nuna mutun kurma ne, a kwai wasu ma da dama.

An tabbatar da cewar za’a fitar da alamomin ne idan Allah ya kai rai nan da watan gobe, mutane masu wayoyin Apple da ma masu sauran wayoyi zasu iya saukar da su a wayoyin su.