TARABA: APC Tana Zargin Gwamnatin PDP Da Amfani Da Sarakunan Gargajiya Domin Kama Kafa.....

Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban jam'iyyar APC Alhaji Jika Ardo ne yayi zargin cewa gwamnatin jihar ta PDP tana rabawa sarkanun gargajiya kudi su kama mata kafa kan shari'ar da aka kai gaban kotun zabe.

Shugaban jam'iyyar APC mai adawa a jihar Taraba, Alhaji Hassan Jika Ardo, yayi zargin Gwamnatin PDP mai ci a jihar da cewa tana rabawa sarakunan gargajiya kudi suna bi ciki da wajen jihar suna kama kafa kan karar da APC ta shigar gaban kotun sauraron kararrakin zabe suna kalubalantar zaben Gwamna.

Shugaban jam'iyyar ya gayawa wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz cewa, kama kafar ta kai har ga mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa'ad na III, domin su kuma su yiwa shugaba Muhammadu Buhari magana.

Alhaji Ardo, yace idan gwamnatin jihar tana da kwarin guiwar cewa ta ci zabe, me yasa take kama kafa. Wannan a cewarsa ya kara tabbatar da abunda suke zargin cewa aringizon kuri'u ne aka yi ba zabe PDP taci ba.

Amma da yake maida martani, wani hadimin Gwamnan jihar Darius Isiyaku Alhaji Abubakar Bawa, yace wannan yarfe ne irin na 'yan adawa, kuma idan wasu suna neman suna, suyi ta yi, amma su basu da wata fargaba.

Alhaji Bawa, yayi kira ga 'yan hamayya da sauran jama'ar jihar, su zo su hada kai domin ciyar da jihar gaba.

Tunda farko, sai da jami'an tsaro suka yi da gaske sannan suka kubutar da tsohon mukaddashin gwamnan jihar, wanda yanzu senata ne, Alhaji Sani Abubakar Danladi na PDP, wanda yara suka so yi masa kofar rago da ya zo gaban kotun sauraron kararrakin zabe domin bada bahasi kan kalubale da Sani kona, yake yi kan zaben tsohon mukaddashin gwamnan a zaman senata karkashin tutar PDP.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

kotun zabe a Taraba