APC Ta Tsayar Da Dan Takararta A Borno

Dan Takarar Jam'iyyar APC Farfesa Babagana Umara Zullum

A zaben fidda gwani na masu takarar gwamna na APC da aka yi a jihohin Borno da Yobe Farfesa Babagana Umara Zullum na Borno da Mai Mala Boni na Yobe, mutanen da tun farko suke da goyon bayan jam'iyyar, suka ci nasara.

Malam Ahmed El Manzur wanda uwar jam'iyyar APC ta tura Borno domin gudanar da zaben fidda dan takarar gwamnanta a jahar shi ya bayyana sakamakon zaben.

Ya bayyana Farfesa Umara Zullum a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 4433. Wanda ya zo na biyu kuri'u 114 kacal ya samu.

Kafin zaben, mutane 10 suka janye daga takarar cikin su 21 dake neman kujerar tare da yin alkawarin marawa Farfesa Babagana Umara Zulum baya a zaben na badi.

Da yake magana, Farfesa Zullum ya ce samun zaman lafiya ya sa gaba, domin idan babu zaman lafiya ba za'a samu ci gaba ba. Sai da tsaro zai iya gina jihar. Abun dake biye da samun zaman lafiya su ne ayyukan ci gaba irin ruwan sha, hanyoyin sufuri da ilimi wajen gina makarantu.

Tun farko dai gwamnan jihar Kashim Shettima ya bayyanawa jama'a cewa Farfesa Umaru Zulum ne dan takarar da suka amince dashi.

Hakazalika a jihar Yobe Alhaji Mai Mala Boni wanda tun farko jam'iyyar ta fitar shi ya zama zakara.

A saurari rahoton Haruna Dauda Biu

Your browser doesn’t support HTML5

Farfesa Umar Zulum Shi Ne Dan Takar Gwamnan Borno Na APC - 3' 08"


ONI