APC Ta Lashe Zabukan Gwamna Na Jahohin Borno Da Yobe

  • Ibrahim Garba
    Haruna Dauda Biu

Taswira mai nuna jahar Borno ta kuryar gabashin Najeriya

Yayin da 'yan jam'iyyar APC ke cigaba da shagulgulan nasarar zabe a jahar Borno, wasu 'yan PDP na ganin da kamar wuya a ce dinbin wadanda su ka yi rajista sun fito sun kada kuri'a kamar sam babu wanda ya mutu ko kuma ya kaura.

Sakataren jam’iyyar APC, Alhaji Mai Mala Buni ya ci zaben gwamnan jahar Yobe da kuri’u 444,013, bayan ya doke abokin karawarsa Ambassada Umar Iliya Damagum, wanda ya samu kuri’u 95,703. Dayake bayyana sakamakon zaben, babban baturen zaben jahar, Furfesa Abubakar Musa Kunduri, Alhaji Buni ya cika dukkannin ka’idoji don haka ya ayyana shi a zaman wanda ya ci zaben. Alhaji Buni ya yi kira ga Alhaji Kunduri da ya zo su hada kai su ciyar da jahasu gaba tare.

A jahar Borno ma jam’iyyar APC ta lashe zaben gwamna, bayan da dan takararta Furfesa Babagana Umara Zulum ya ci kuri’u 1,175,440 ya doke dan takarar jam’iyyar PDP Alhaji Muhammad Alkali Imam, wanda ya samu kuri’u 66,115. Da ya ke bayyana sakamakon zaben, Furfesa Alhassan Gani na hukumar INEC ya ce Zulum ya cika ka’idojin da su ka wajaba saboda haka ya ayyana shi a matsayin gwamnan jahar ta Borno. Furfesa Gani ya an gudanar da zaben a fadin jahar Borno lafiya in banda dan rikicin da aka samu a karamar hukumar Hawul wanda ya kai da soke wasu kuri’un wadanda yawansu bai kai yadda zai shafi sakamakon zaben ba.

To sai dai jam’iyyar PDP ta ki rattaba hannu kan sakamakon zaben. Kwamrad Umar Bello, Sakataren tsare-tsaren jam’iyyar PDP ya ce sun ki sa hannu a sakamakon zaben ne saboda da alamar an tafka rashin gaskiya. “

Ga wakilinmu Haruna Dauda da cikakken rahoton. Ya ce, “a duk inda ake zabe a duniya da wuya kashi 70 cikin dari na wadanda su ka yi rajista su kada kuri’a; sai gashi a wannan zabe har kashi casa’in da tare ko kashi casa’in da takwas na wadanda su ka yi rajista su ka yi zabe. Wannan na bukatar dubawa -- cewa ba wadanda su ka mutu, ba wadanda su ka kaura.”

Ga wakilinmu Haruna Dauda da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

APC Ta Lashe Zabukan Gwamna Na Jahohin Borno Da Yobe