Sakataren Jamiyyar APC Maimala Buni, ya ce shugabannin jam'iyyar sun yi alkawalin ganin jam'iyyar ta yi rawar gani a zaben 2019, wanda hakan ne yasa suka tashi haikan domin dinke barakar da aka samu a jam'iyyar.
Buni ya ce basu fargabar wata barazana ga abin da suka sa a gaba kuma suna sa ran yin nasara.
" An ce duk juma'ar da za ta yi kyau tun da daga Laraba ake ganewa," inji Maimala.
To ko tawagar su Buba Galadima za su dawo jam'iyyar? Buni ya ce shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa bai yiwuwa a kulle kofa ga 'ya'yan jam'iyyar saboda haka kofa a bude take domin a yi sulhu.
"Ba yadda jam'iyya za ta yi karfi ta gawurta, a ce kuma ba ta da matsala," babban sakataren ya fada. A cewarsa, "matsalar ba za ta hana ci gaba ba."
Sai dai shi Buba Galadima ya ce akwai abin dubawa kan yadda ake gudanar da jam'iyyar.
" Akwai korafe-korafe, mutane da yawa sun je kotu, ba a yi adalci ba, ba a nuna gaskiya ba yadda aka fidda shugabannin wannan jam'iyya, " inji Buba Galadima.
Ya ce a matsayinsu na wadanda suka kafa jam'iyyar, tilas ne su fito su yi gyara. A cewarsa, "Wannan yaki na gyara wannan jam'iyya shine suka sa a gaba kuma in Allah ya yarda zamu tabbatar da shi don muke da goyon bayan al'umma kuma al'umma sun yarda da abun da muke yi ba don kanmu muke ba."
Saurari rohoton
Your browser doesn’t support HTML5