APC Na Shirin Gudanar Da Zaben Fidda Gwani Da ‘Yan Takara 23

APC

Jam’iyyar APC mai mulki a tarayyar Najeriya na shirin gudanar da zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa da ‘yan takara 23.

Matukar jam’iyyar ba ta kawar da wasu daga ‘yan takarar ba a tantancewa da ta ke yi yanzu, za ta gudanar da zaben ranar litinin da mafi yawan ‘yan takara a tarihi.

‘Yan takarar sun hada da gwamnoni masu ci, tsoffin manyan jam’ian siyasa, mataimakin shugaba Yemi Osinbajo, jagoran jam’iyya Bola Tinubu da sauran su.

Muhawarar da cewa ko akasin ta, ta takarar, ta fi yawa a tsakanin magoya bayan Bola Tinbu da Yemi Osinbajo.

Shugaban nazarin kamfen din bangaren Tinubu, tsohon sakataren gwamnati Babachir David Lawal ya bugi kirjin za su lashe zaben fidda gwanin.

A kudu maso yamma akwai ‘yan takara da dama da su ka hada da gwamna mai ci Kayode Fayemi na jihar Ekiti da ‘yan kamfen din sa irin su Tijjani Tumsa ke nuna in a na batun cancanta ne ba za a tsallake su ba.

Duk da alamun karkatar APC ga fitar da dan takara daga kudu amma akwai ‘yan arewa da su ka hada da gwamna Yahaya Bello na Kogi da Abubakar Badaru na Jigawa da ke cikin takarar.

Ba a ga tsohon shugaba Jonathan a zauren tantance ‘yan takarar ba, duk da bayanan da ke nuna ya na cikin jerin ‘yan takara kuma kotu ma ta share ma sa hanyar takarar.

APC za ta gudanar zaben fidda gwanin a ranar litinin mai zuwa a dandalin EAGLE da ke Abuja.

Saurari cikakken rahoton cikin:

Your browser doesn’t support HTML5

APC Na Shirin Gudanar Da Zaben Fidda Gwani Da ‘Yan Takara 23