Dan takarar Shugabancin Najeriya na jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari (murabus) ne ya yi galaba a zaben shugaban kasar a jiahr Adamawa. Wakilinmu a shiyyar Adamawa Ibrahim Abdul’aziz ya ce sakamako daga kananan hukumomi 19 sun nuna cewa Buhari ya ci kananan hukumomi 12 a yayin da Shugaba Goodluck Jonathan ya samu 7.
Abdul’aziz ya ruwaito babban jami’in bayyana sakamakon zaben Furfesa O. Geoffrey Okogbaa Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Wukari, y ace wakilan jam’iyyun sun ba da hadin kai sosai lokacin harhada sakamakon zaben. Y ace duk da yak e akwai wasu kananan hukumomin da har zuwa lokacin bas u samu gabatar da nasu sakamakon ba, abubuwa na gudana da kyau. Y ace da zarar an samu sakamakon sauran kananan hukumomin, za a bayyana komai.
To saidai a jihar Taraba, an dan damu hargitsi a garin Takum game da sakamkon zaben . Ibrahim ya ruwaito wani ganau na cewa sojoji na ta daukar matakan tsaro a yayin da jama’a kuma kowa ke ta kansa saboda gudun abin da zai biyo baya. Ganau din ya gaya ma Ibrahim cewa musabbabin harbeharben da sojoji ke yi shi ne yinkurin murde zaben da jam’iyyar PDP da ta sha kaye ke yi. Don haka sai jami’an tsaro su ka dau mataki. To amma da wakilinmu ya tuntubi jami’in yada labarai na ‘yan sanda jihar Taraba ASP Joseph Kuje y ace bas hi da wannan labarain , kuma a iya saninsa babu wani abin da ya faru a Takum.
Your browser doesn’t support HTML5